3 Jul 17, 09:08 PM, Africa/Lagos | Previous 7 of 7 Next

Allah ya yi wa Dan masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule rasuwa a ranar Litinin da safe bayan ya sha fama da jinya. Wata majiya daga iyalansa ta tabbatarwa da BBC rasuwar, amma babu wani karin bayani zuwa lokacin wallafa wannan labari. Ya rasu ne a kasar Masar inda ya yi jinyar rashin lafiyar da ya yi fama da ita. Marigayi Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya. Dan masanin Kano ya mutu yana da shekara 88

Comments

Drop a comment on this picture

Hi! You need to register to leave a comment on this post | Register
title:
body: